Connect with us

Labarai

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nemi Ganduje ya bada damar yin sallah a Kano

Published

on

Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Global Community for Humman Right Network, Kwamred Karibu Yahya Lawan Kabara, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta bawa al’ummar jihar damar da za su je masallatai su rinka yin sallar Juma’a domin rabauta da Rahamar Allah S.W.T.

A zantawar sa da gidan rediyon Dala yau Talata a ofishin kungiyar, shugaban kungiyar, Kwamrade Karibu ya ce” Matukar za a bude kasuwanni a ranakun Litinin da Alhamis mutane su je su yi siyayyar kayayyakin abinci da na masarufi, babu shakka yakamata a bawa mutane damar da za su je su yi sallar Juma’a ko da kuwa muntuna goma sha biyar ne, idan za su yi su bada tazara, bisa muhimmancin da sallar take da shi”.

Ya kuma ce” Kamata ya yi gwamnatin jihar dama kasa baki daya, ta yi koyi da kasar Saudiyya wajen yin Sallar Juma’ar harma da sallolin nafila, domin neman afuwar Allah S.W.T daga cutar Covid-19. Yanzu haka kungiyoyin mu na kare hakkin dan Adam sun fara shirye-shiryen gabatar da wanda ya fara zuwa Kano da cutar Covid 19, bisa sakacin da ya nuna lokacin da ya shigo da cutar jihar”. Inji Kwamrade Karibu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Karibu Yahya Kabara ya kara da cewa, bai kamata a kyale wanda a kai zairgin shi ne a ke zargin ya fara shigo da cutar jihar Kano ba, domin dokar kasa ce ta tanadi biwa ‘yan kasa hakkin su ga wanda ya shigo mu su da wani ciwo mai yaduwa, har ya bazu a gari, bayan kuma ya san ya na dauke da ciwon.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending