Connect with us

Labarai

Ba za mu yarda a yi taron Idin Kwakwa ba a wannan lokaci -‘Yan Sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi wata ganawa ta musamman da ‘yan kwamitin masallacin Abdullahi Suka dake garin Zawaciki dake yankin karamar hukumar Kumbotso da kuma Dagacin yankin bisa yadda a ke gudanar da al’adar taron jama’a a masallacin wanda a ke wa lakabi da idin Kwakwa bayan sallar Idi wanda ‘yan mata da samari ke taruwa.

Baturen ‘yan sandan yankin Muhammad Talba ne ya jagoranci zaman ganawar a yunkurin hukumar na dakatar da cunkuso domin dakile yaduwar cutar Corona a fadin jihar da ma kasa baki daya.

A nasa bangaren limamin masallacin Abdullahi Suka, Alhaji Muhammad Sabi’u Zawaciki kiran mutane ya yi da su kiyaye bin dokokin da a ka sanya wajen gudanar da sallar Idin.

Da yake jawabi yayin ganawar Malam Alhassan Ibrahim wanda shi ne shugaban kwamitin masallacin ya bayyana cewar” Za mu ja hankalin mutane yayin gudanar da huduba ba saye babu siyarwa kowa ya na idar da sallar Idin kowa ya koma gida domin kiyaye dokar da a ke ciki ta zaman gida”.

Shi ma Dagacin yankin, Alhaji Abdulkadir Mu’azu Zawaciki ya kara baiwa al’umma hakuri cewa” Ku daure ku bi dokokin, domin komai sai da lafiya a ke yin sa kuma addinin ma haka ya koyar”.

Wakilin mu Sayyadi Haruna Kutama ya ruwaito cewar ma su ruwa da tsaki a kan lamuran masallacin sun bayyana cewa za su yi iya yin su wajen ganin an bi dokokin yadda ya kamata.

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!