Connect with us

Labarai

‘Yan sanda a Kano sun cafke ‘yan Kaduna 120 da suka shigo Kano a yayin Corona

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tace ta cafke mutane 120 da suka shigo jihar Kano daga jihar Kaduna dukda dokar kulle da aka sanya a jihohin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Habu Ahmed Sani ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a yammacin Alhamis dinnan.
Kazalika Kwamishinan ya kara da cewa sun kuma cafke mutoci 74 da baburan adaidaita sahu 45 sai kuma babura masu kafa biyu guda 50.
Kazalika an cafke mutane da suka shigo Kano daga sauran jihohi da suka hadar da Kaduna, Katsina, Bauchi da kuma Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sandan na Kano ya ce tuni suka gurfanar wadanda suka kama a gaban kotun tafi da gidanka da gwamnatin Kano ta samar domin hukunta masu bijirewa dokar.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar Rundunar Yansandan ta gargadi da su gujewa karya dokar kulle da zaman gida domin kaucewa fadawa komar ‘yan sandan.

Labarai masu alaka:

Al’ummar Kano ku sanya makarin baki na Face Mask a lokacin sallar Idi -Civil Defence

Covid-19: Yadda gwajin Corona ke tafiya a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish