Connect with us

Labarai

‘Yan sanda a Kano sun cafke ‘yan Kaduna 120 da suka shigo Kano a yayin Corona

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tace ta cafke mutane 120 da suka shigo jihar Kano daga jihar Kaduna dukda dokar kulle da aka sanya a jihohin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Habu Ahmed Sani ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a yammacin Alhamis dinnan.
Kazalika Kwamishinan ya kara da cewa sun kuma cafke mutoci 74 da baburan adaidaita sahu 45 sai kuma babura masu kafa biyu guda 50.
Kazalika an cafke mutane da suka shigo Kano daga sauran jihohi da suka hadar da Kaduna, Katsina, Bauchi da kuma Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sandan na Kano ya ce tuni suka gurfanar wadanda suka kama a gaban kotun tafi da gidanka da gwamnatin Kano ta samar domin hukunta masu bijirewa dokar.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar Rundunar Yansandan ta gargadi da su gujewa karya dokar kulle da zaman gida domin kaucewa fadawa komar ‘yan sandan.

Labarai masu alaka:

Al’ummar Kano ku sanya makarin baki na Face Mask a lokacin sallar Idi -Civil Defence

Covid-19: Yadda gwajin Corona ke tafiya a Kano

Labarai

Masu koyarwa a aji su ci gaba da zama a gida – KSSSMB

Published

on

(more…)

Continue Reading

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish