Connect with us

Labarai

Ba da dama da gwamnati ta yi a yi sallar juma’a a Kano ya yi daidai -Human Right

Published

on

Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Global Cummunity for Humman Right Network, Karibu Yahya Lawan Kabara, ya ce matakin da gwamnatin Kano ta dauka na bada dama a rinka yin sallar Juma’a a lokacin cutar Covid-19 ya yi dai dai.

Karibu Kabara ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala yau Juma’a a ofishin sa dake unguwar Sharada.

Ya ce”Za mu zagaya masallatai domin ganin al’umma ko za su bi sharudan da a ka kafa na yin amfani da matakan kariya a yayin da za a yi sallar ko akasin hakan. Al’umma su bi shawarwarin likitoci wajen sanya takunkumi a fuskar su yayin da za su fita waje tare da bada tazara wajen gudanar da mu’amular su da mutane”. Karibu Kabara.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Shugaban Kungiyar kare hakkin dan Adam, Karibu Kabara ya kuma shawarci al’umma cewar, matukar su ka ga wani canjin yanayi a tare da wani mai kama da cuta mai sarkewar numfashi ta Covid-19, za su yi kokarin kiran lambar da a ke bayarwa ta karta kwana domin daukar matakin da ya dace domin kaucewa ta’azzarar cutar Coron virus.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish