Connect with us

Labarai

Mu rubanya ayyukan da mu ka yi a watan Ramadan domin dacewa da rahamar Allah -Liman

Published

on

Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na Abubakar Dan Tsakuwa dake Ja’en Yamma Ring Road by Pass a karamar hukumar Gwale, Mallam Ibrahim Musa Alharazimi, kira ya yi ga al’ummar musulmai da su kara rubanya ayyukan da su ka gudabanar a cikin watan Azumin Ramadana bayan watan ya wuce, domin rabauta da rahamar Allah (S.W.T.).

Mallam Ibrahim Musa ya yi kiran ne jim kadan bayan kammala hudubar Juma’a da ya gudanar a masallacin, wanda ta mayar da hankali a kan rubanya ayyukan alkhairi a bayan watan Ramadan.

Ya ce” Matukar mutane za su kara rubanya ayyukan alkhairi su kuma kaucewa aikin alfasha, babu shakka za su yi dace da rahamar Allah (S.W.T) ya ke rabawa ga muminai. Sannan kuma mutane su rinka bin shawarwarin likitoci na sanya takunkumin rufe fuska tare da bada tazara a tsakanin juna, domin kaucewa kamuwa da cuta mai sarkewa numfashi ta Coronavirus”. Liman Ibrahim

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, al’umma da dama ne su ka halarci masallacin a karo na farko tun cikin sati biyar da ba a yi sallar Juma’ar ba, sakamakon bullar cutar Coronavirus a jihar Kano.

Labarai

Zaman lafiya: Majalisar dinkin duniya ta taka rawa – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce majalisar dinkin duniya, ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar tunawa da majalisar dinkin duniya a wannan shekarar.

Ya ce, “Nijeriya ta zama mamba ce a majalisar ta dinkin duniya a 1960 a matsayin mamba ta 99”. Inji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Continue Reading

Labarai

Polio: Za mu dakile bullar cutar shan inna a Kano – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da sanya idanu, domin ganin ba a sake samun bullar cutar shan inna ba ta Polio a fadin jihar Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a wani bangaren na bikin ranar yaki da cutar shan inna ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da rigakafin cutar Polio a fadin jihar Kano, duk da cewa babu cutar a jihar wanda hakan zai bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar a nan gaba”. A cewar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Sai dai ya bukaci iyaye da su ci gaba da kai yaran su, domin karbar rigakafin wanda hakan ne kadai zai taimaka wajen yaki da cutar ko da a nan gaba.

 

Continue Reading

Labarai

‘Yan sandan SARS 16 za su fuskanci hukunci sakamon zargin kisan kai

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin ya yi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.

Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.

Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Lagos da Ogun, Rivers, Gombe, Kaduna da Kogi da kuma Kwara.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!