Connect with us

Manyan Labarai

Premier League: Leroy Sane zai bar Manchester City -Pep Guardiola

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola, ya tabbatar da cewa dan wasan kungiyar kuma dan kasar Jamus, Leroy Sane zai bar kungiyar kwallon fata ta Man City a wannan kakar.

Guardiola ya ce dan wasan Sane mai shekaru 24 kwantiragin sa zai kare a wannan shekarar sai dai kuma yaki rattaba sabon kwantiragi wanda tun a shekarar bara ya nuna sha’awar sa ta komawa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich.

Sai dai a cewar Guardiola ya ce” ban san ko zai bar kungiyar mu a wannan kakar ba ko kuma wata kakar, amma tabbas ya na son komawa wata kungiyar”. Guardiola.

A shekarar 2016 ne dan wasan Sane ya koma kungiyar Manchetser City daga Schalke ta kasar Jamus a kan kudi Fam miliyan 37 tsawon kwantiragin shekaru 5.

Dan wasan bai dai doka wasa ko daya ba tun watan Agusta sakamakon raunin da ya samu a kafar sa a gasar cin kofin Cmmunity Sheild.

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta zargin gididdiba burtalai a wasu garuruwan ta uku

Published

on

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta batun gididdiba burtalai a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, dukka a ƙaramar hukumar da ake zargin an siyarwa Manoma, domin suyi aikin Noma.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan a daren jiya Laraba, lokacin da yake tsokaci kan koken da Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka yi, kan yadda suka zargi an gididdiba burtalai a yankunan su, an siyarwa wasu Manoma, domin suyi aikin Noma, lamarin da suka ce hakan barazana ce a gare su.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu wajen gididdiba burtalai a garuruwan, yana mai cewa ko da kansilolinsa daga zuwan su bai taɓa sanin wanda ya siyar da koda kuwa kunya ɗaya ba a cikin shugabancin sa na ƙaramar hukumar domin ayi Noma, haka shima bai siyar ba.

“Yanzu haka ana kan ɗaukar matakin doka akan waɗanda suka fitar da al’amarin, kasancewar maganar tana wajen ƴan sanda, kuma ana faɗaɗa bincike, “in ji shi”.

A ziyarar gani da Ido, da tashar Dala FM Kano, ta kai wasu daga cikin burtalan da aka yi zargin an siyarwa Manoman, ta iske yadda wasu mutane suke share guraren, kamar yadda suka shaida cewa waɗanda aka siyarwa ne suka basu aikin share wajen.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da wasu Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka koka, bisa yadda suka ce an gididdiba burtalai a yankunan su, duk da wani manomi yace har takarda aka bashi bayan an siyar masa, lamarin da ya sa su cikin damuwa bisa yadda hakan ka iya sanyawa su rasa guraren da za su yi kiwon Shanun su.

Continue Reading

Trending