Connect with us

Labarai

Mu rubanya addu’a a kan halin da Nijeriya ke ciki- Liman

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Abdullahi Bin Mas’ud dake unguwar Kabuga ‘yan Azara, Malam Zakariya Abubakar ya ce, hakuri shi ne babban abinda al’umma ya kamata su yi a wannan lokaci da aka fi watanni hudu ana fama da cutar Corona, da ta haddasa yunwa da karayar arziki, sai kuma kashe-kashen mutane da ake yi a wasu daga cikin jihohin arewa.

Malam Zakariya ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gabatar a masallacin na Abdullahi Bin Mas’ud.

Ya na mai cewa, “Allah Ya umarce mu da mu yi hakuri, kuma dama ya ce, zai jarrabi bawa a kan abubuwa guda biyar, tsoro, yunwa, karayar tattalin arziki, noma, da kuma kashe-kashen rayuka, sai kuma a yi wa ma su hakuri bushara, wadanda idan ya jarabce su za su ce, inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”. A cewar Malam Zakariya.

Ya kara da cewa, “Abun da a ke bukata wajen al’umma a yanzu shi ne hakuri a bisa wannan masifa, mu yi hakuri a kan ibada, da kaddara, sannan mu koma zuwa ga Allah, kuma kada mu yi fushi”. Inji Liman

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewar, Malam Zakariya ya kuma ja hankalin shugabanni akan rike amanar al’umma, wajen tsaron Najeriya, domin dakile kashe-kashen da ake fama da shi a halin yanzu.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending