Connect with us

Labarai

Leda uku ta ruwa ta farfado da wata mata da a ka rataye

Published

on

Ana zargin wasu makwabtan wata mata Marfu’a Mukhtar da rataye ta ranar Asabar din makon da ya gaba ta a unguwar Bubbugaje gidan Jakada dake kamar hukumar Kumbotso.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe goman daren ranar, inda aka yi zargin mutanen guda biyar mata biyu da maza uku sun shiga gidan matar, su ka kuma yi amfani da igiyar guga wajen rataye ta a tagar dakin ta.

Bayan an kai ta asibiti tasha ledan ruwa uku ta farfado farfado, Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya zanta da ita tana mai cewa, “Makwabta na ne guda biyu da muke rigima da su, suka zo su ka kwankwasa min kofa su ka ce sun zo mu yi sulhu, ina bude kofa matan biyu suka shigo tare da maza guda uku, matan suka yi dariya suka fita, mijin kwabciyar tawa  ne ya bani waya ta ya ce, in kira ‘yan uwana su ceto ni, tunda kome zan yi sai na kira waya, shi ne na kira Abdullahi abokin mijina, sai suka yanki igiyar guga suka nada min a wuya suka rataye min wuya har na fita daga hayyacina. Ni dai abin da nake bukata shi ne mahukunta su bi min hakkina”. A cewar Marfu’a.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron dinki ya zanta da mahaifin Marfu’a, Malam Mukhtar Muhammad dake Dorayi Chiranci, inda Ya ce, “Lokacin da abin ya faru wajen karfe goma na dare aka bugo min waya aka ce Marfu’a an rataye ta, gaba daya hankalin mu ya tashi, shi ne na tura wasu su je, saboda matasa sun tafi da makamai, kada su bari yaran su sari kowa, domin kada a bari su dauki doka a hannu, kuma ana zuwa aka ga an rataye ta. Inji Malam Mukhtar.

Kazalika, mijin Marfu’a Sani Isma’il Ya ce, “Na bar cajin waya ta mata ta ta kira wayar ta ba ta samu ba, sai ta kira lambar abokina, sai makwabtan nawa suka afka mata, kuma ko a ofishin ‘yan sanda sun yi barazanar sai sun kashe ni kuma bamu san abin da mu ka yi mu su ba”. A cewar Sani Isma’il.

Shi ma wanda ya ceto Marfu’a, Abudllahi Muhammad Wada,  ya magantu da cewa, “Ni ne farkon wanda na fara zuwa gidan nata, da ta kira ni na daga wayar, sai naji an kwace wayar, na kira mijin bai daga ba, ina zuwa na shiga naga an rataye ta, sai na dauke ta a hoto saboda shaida.”  Inji Abdullahi Muhammadu.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, mun yi kokarin jin ta bakin wadanda ake zargi amma basu magantu ba, saboda suna hannun ‘yan sanda, inda kuma Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar hannu ya shaida cewar sun samu labarin faruwar al’amarin amma bai yi martani ba.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending