Connect with us

Labarai

Hanyoyin da za a bi wajen gudanar da aiki a kotu

Published

on

Kotunan Majistri Arba’in da Hudu da ke rukunin kotunan Nomansland a Kano sun koma bakin aiki ka’in da na’in, sakamakon umarnin da babban jojin jihar Kano, Mai Shari’a Nura Sagir Umar ya bayar a kan bude kotunan, tun bayan cire dokar kulle.

Kakakin kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan a zantawar su da gidan rediyon Dala da a Litinin dinnan.

Ya ce, “Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar da ta sanya ta hana zirga-zirga, ta kuma yi umarnin ma’aikata su koma bakin aiki, bisa tsarin lokacin zuwa da kuma lokacin tashi, hakan ya sanya babban jojin jihar Kano ya umarci dukkan alkalan kotunan majistri da su koma bakin aikin su, a wannan rana ta Litinin 06-07-2020, kuma komawar ba za ta zama daidai da irin ta da ba, akwai ka’idojin saka abun rufe baki da fuska, akwai kuma man wanke hannu, da kuma bayar da tazara a tsakanin mutane”.

Ya kuma kara da cewa, “A baya kotuna ne guda uku ke aiki a lokacin hana zirga-zirga, domin karbar karar kulawar gagggawa, yanzu kuma tun da an janye dokar, a ka umarci kowanne alkali dake kotun majistri ya koma bakin aiki”. A cewar Baba Jibo.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Baba Jibo ya kuma ce, wadanda kararrakin su sun riga sun wuce lokacin da a ka ba su, za su koma kotunan ne domin sabun ta mu su wasu lokutan, wadanda kuma sababbin kararraki ne za su shigar, a yanzu su na da cikakkiyar damar da za su shigar da kararrakin su bisa tsarin da a ka sanya.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending