Connect with us

Labarai

Al’umma su yi hakuri da matsin rayuwa – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Masjidul Quba da ke unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni, Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya ce, al’umma su yi hakuri da halin matsin rayuwa sakamakon bullar cutar Corona.

Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana hakan ne a hudubar sa ta juma’a da ya gudanar a masallacin.

Ya ce, “Hadisin manzon Allah (S.A.W) ya na cewa, lamarin mumini abun ban mamaki ne, idan farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah, ba zai rinka nuna cewar ya isa ba ne, haka kuma idan abun sosa rai ya same shi sai ya yi hakuri, annabi ya ce in ba mumini ba babu mai yin wannan”.

Limamin, ya kuma ce, “Jama’a mun samu kan mu a cikin matsatsi, domin haka alkur’anin madaukakin sarki ya ke bayanin irin nau’i-nau’i na yadda in ka samu kan ka cikin halin da mu ke ciki za ka hakurtar da kan ka, na farko ka san yadda rayuwar duniya ta ke da dadi da wahala. Idan ka na cikin dadin kada ka dauka za ka tabbata a kan haka, idan kuma ka samu akasin haka kada ka dauka zaka dawwama a haka”.

Ya kara da cewa, “Wannan Corona ta sanya an rufe mutane, wani sai ya fita zai samu abun da zai ci ya kawo wa iyalin sa an rufe an ce kada ya fita, wani ma ya na kasuwancin ya lalace, wani kuma bashi da lafiya an ki karbar sa a asibiti, saboda haka idan mutum ya samu kan sa a wannan yanayi ya koma ga Allah shi ne magani”. A cewar Malam Ibrahim Tofa.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewa, Malam Ibrahm Abubakar Tofa, ya kuma ja hankalin mutane da su ci gaba da gudanar kasuwanci cikin neman halak, maimakon tara abun duniya ta kowanne hali.

 

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending