Connect with us

Labarai

Mun dawo da ‘yan Najeriya sama da 6000 gida – Gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta ce ‘yan kasar da annobar korona ta rutsa da su a kasashen ketare, 6,317 ne aka mayar da su gida.

gwamnatin kasar ta ce mutanen an kwaso su ne daga kasashe 21, ciki har da Amurka, Burtaniya, Saudiyya, Masar da kuma Faransa.

Sauran kasashen sun hada da: Indiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiyya, Sudan, Kenya da kuma Senegal.

Shugabar hukumar lura da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

Jawabin nata ya zo ne a matsayin wani bangare na shirye-shiryen bikin ranar ‘yan Najeriya mazauna ketare, wanda zai gudana ranar 25 ga watan Yulin 2020.

Dabiri Erewa ta ce baya ga mutanen da aka kwaso saboda annobar Korona, akwai kuma wasu ‘yan Najeriyar da aka kwaso daga kasar Afirka ta Kudu a watan Satumbar 2019, wadanda rikicin kin jinin baki ya rutsa da su.

Labarai

Rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi – Masanin tattalin arziki

Published

on

Wani masanin tatttalin arziki a jihar Kano Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, ya ce rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) kwandaloli, hakan kan haifar da koma baya musamman ma ga ƙasashen da basa amfani da su.

Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, wanda kuma shine shugaban sashin koyar da ilimin banking and finance na jami’ar tarayya ta Dutse, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Doka Gatan Al’umma na nan gidan rediyon Dala FM Kano, da ya gudana a yau Litinin.

“Dai na amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi, kuma idan mutum yaje sayen kayan masarufin zai fuskanci hakan, “in ji Dr. Ibrahim”.

Ya ƙara da cewa duk da cewar dai na amfani da ƙananun kudaɗen (Coins) da zarar an inganta harkar wutar lantarki, babu makawa za’a samu sauƙi saboda masu ƙananun masana’antu za su rage kashe kuɗi.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa Dakta Ibrahim Muhammad Ahmad, ya kuma bukaci hukumomi da su mayar da hankali akan noma da sanya kishin kasa a gaba, domin samar da ci gaba ga al’umma.

Continue Reading

Labarai

Zamu magance ƙalubalen da ake samu a fannin ilimi mai zurfi – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta sha alwashin mangance dukkanin wani ƙalubale a fannin ilimi mai zurfi a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Ibrahim Yusif kofar mata, ne ya
bayyana hakan a yayin taron yaye daliban kwalejin ilimi ta Aminu
Kano (AKCOE), da ya gudana a ranar Alhamis.

Y kuma ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa a hukumance akan bukatar kwalejin dan ganin ta samu wadataccenf ilin da za ta gina jami’a.

Dakta Ibrahim kofar mata ya bayyana gamsuwa da tsarin da kwalejin take bi wajen gudanar da karatu, inda ya kuma ja hankalin dalibai 40 da suka karbi shaidar kammala karatun NCE,
da su zama ababen koyi.

Da yake nasa jawabin shugaban kwalejin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce da zarar sun shiga sabon tsari za su fara da daukar dalibai yan asalin jahar Kano mutum dubu daya kyauta, tare da biyawa ‘yan makarantar
kudi sama da Naira miliyan 300 yan asalin jahar kano dan
karfafawa matasa gwiwa.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron daga guraren daban-daban na jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Trending