Connect with us

Labarai

Kuskure ne cinye naman layya ba’a bayar da kyauta ba – Aminu Kidir

Published

on

Wani malamin addinin musulunci a jihar Kano Malam Aminu Kidir ya ce, al’ummar da Allah ya basu damar yin layya to su taimakawa mabukata, maimakon su tattare naman su cinye su kadai a gida.

Malam Aminu Kidir ya bayyana hakan ne ta cikin Doka Gatan Al’umma na gidan rediyon Dala a ranar Alhamis.

Ya ce, “Ba daidai ba ne mutum ya yi layya ya cinye naman bai yi kyauta da wani bangare ba a cikin sa ba, domin an so a raba naman gida uku a yi kyauta da kaso daya, kaso daya kuma a bayar sadaka, sauran kuma a ci a gida”.

Ya kuma ce, Ba’a a yin layya da gurguwar dabba, ko mai harara garke, ko kuma makauniya, sai kuma dabbar da ba ta da lafiya, saboda haka a na son a yi layya da kosasshiyar dabba maimakon ramamme, kuma an fi son a yanka mai launin fari da baki, zagayen idanun sa da bakin sa da kuma kafafun sa bakake.

Ya kara da cewa, “Lokacin da a ke son a fara layya shi ne lokacin da a ka idar da sallar idi, liman ya yanka dabbar layyar sa, kuma an fi son a yi kafin sallar Azahar, kuma sai an yi kwana uku a na yin layyar, duk wanda bai yi a wannan kwanakin ba, ba layya ya yi ba nama ya ci”. A cewar Malam Aminu Kidir

Malam Aminu Kidir ya kuma ja hankalin masu karbar bashin layya kuma basu da ikon biya a kan lokaci, da su yi hakuri, domin layya tana hawa kan mutumin da yake da wadatar yi ne.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending