Connect with us

Labarai

HAR YANZU WASU DAGA CIKIN SANATOCI NA CECE KUCE GAME DA KASAFIN KUDIN BANA.

Published

on

Har yanzu wasu sanatoci na cece ku ce akan kasafin kudin bana wanda shugaba Muhammad Buhari ya riga ya rattabawa hannu.
Sanata mai wakiltar yammacin jihar Nassarawa Abdullahi Adamu ya bukaci a yiwa ‘yan Nigeria bayanai dalladalla, shi kuwa mai wakiltar Gombe ta tsakiyaSanata Danjuma Goje cewa ya yi majalisar na da kwararan hujjoji na yiwa kasafin kwaskwarima.
Har yanzu ana samun takun saka tsakanin ‘yan majalisar dattawan kasar dangane da kasafin kudin 2018, Sanatan dake wakiltar mazabar yammacin jihar Nasarawa Abdullahi Adamu ya ce akwai abun dubawa akan korafin cushe da aka zargi majalisar kasa da yi.
Sanata Abdullahi Adamu yana son shugaban kasa da ofishin dake kula da kasafin kudi su baza kolin abun da aka kawo masu daga majalisar domin a yiwa ‘yan Nigeria cikakken bayani kowa ya gane.
Amma shugaban kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar dattawa Sanata Danjuma Goje ya yi bayanin abun da ya sa suka yiwa kasafin kudin garambawul bayan da shugaban kasa ya mika masu.
Ya ce tashin farashin man fetur a kasuwar duniya na cikin dalilin da ya sa suka yiwa kasafin gyara.
Danjuma Goje yace dama can akwai doka da ta ce kashi daya cikin dari na kasafin kudin kasar za’a tanadarwa kiwon lafiya. A can baya ba’a kiyaye dokar ba amma a wannan karon majalisa ta ga ya dace su yi aiki da dokar.

Labarai

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauya shugaban hukumar tattara haraji na jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dakta Zaid Abubakar, a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano, da kuma Kasim Ibrahim a matsayin babban daraktan hukumar.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da aka aikowa Dala FM Kano, a daren jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban hukumar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, an mayar da shi ne a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari, wanda kuma sauye-sauyen za su fara aiki nan take.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Labarai

Abin takaici ne yadda ake fuskantar ƙarancin ruwan Sha a sassan jahar mu – Gwamnan Kano.

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nuna rashin jin daɗin sa bisa yadda ake samun ƙarancin Ruwan Sha, a wasu daga cikin sassa jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, a lokacin a ya kai ziyarar gani da ido, matatar Ruwa da ke Tamburawa a yammacin yau Juma’a, a ƙokarin sa na na gyara ɓangaren ruwan a cikin garin Kano.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma sha alwashin tabbatar wa al’umma cewar, gwamnatin sa za ta yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da isasshen ruwan Sha ga al’ummar jihar Kano.

Gwamnan ya ƙara da ce a lokacin da suka zo ba sufi mako biyu ba suka samar da ingantaccen Ruwan sha, wanda ya rinƙa shiga cikin lunguna da Sako na sassan jihar.

Continue Reading

Trending