Connect with us

Labarai

Kano: Dalilin da ya sanya a ka kwace kujera a hannun APC

Published

on

Jam’iyyar PDP a jihar Kano ta yi nasarar karbar kujerar dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Rogo, Magaji Dahiru Zarewa na jam’iyyar APC, wanda Jibrin Isma’ila Falgore daga Jam’iyar ta PDP ya zama dan majalisar karamar Hukumar a halin yanzu.

Kotun sauraron korafin zaben dan majalisar dokokin jihar Kano ce ta kwace kujerar daga hannun dan majalisar na jam’iyyar APC ta bai wa jam’iyyar PDP.

Lauyan wanda ya shigar da kara, Jibrin Isma’ila Falgore na jam’iyyar PDP, Barista Ibrahim Garba Waru, a zantawar sa da manema labarai ya ce, “Kotun ta ce, dan takarar jam’iyyar APC bai sauka daga kan mukamin sa ba lokacin da ya samu nasara a zaben da ya gabata”.

Ya kuma ce, “Dukkannin kuri’u da Alhaji Magaji Dahiru Zarewa na jam’iyyar APC ya samu haramtattu ne, saboda haka kotun ta kwace nasarar da ya samu ta bai wa dan takarar jam’iyyar PDP”. Inji Barista Ibrahim

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Trending