Labarai
Mu guji yada hotunan yaran da a ka yiwa fyade – Hajiya Gambo

Shugabar kungiyar wayar da kan iyaye mata da sauran al’umma a kan yadda za’a dakile matsalolin da su ke damun mata, Hajiya Gambo A. Garba ta ce, yawancin fyaden da a ke yadawa a social media ba a jihar Kano a ke yin sa ba, amma a ke dauka a dora a ce Kano a ka yi.
Hajiya Gambo A. Garba ta bayyana hakan ne a zantawar ta da gidan redyon Dala, jim kadan bayyan kammala taron addu’a domin kawo karshen matsalolin da su ka shafi yara, a ranar Litinin.
Ta na mai cewa, “A nazarin da na yi a jihar Kano akwai karancin fyade, amma a social media a nuna mata ace an yi musu fyade, to mu ji tsoron Allah, domin irin wadannan hotuna na kawo karuwar fyade, a taimaka wajen ilimantar da al’umma, a daina barin gwamnati ita ce za ta gyara komai”.
Ta kuma ce,“Idan mutum yaga irin abubuwan nan na fyade a social media, ya goge, domin idan ‘ya’yan mu ne ba za mu yada ba, me yasa za mu rinka yada na wasu? sannan gwamnati ta yi doka a kan masu sayar da maganin gargajiya na maza, domin shima ya na taimakawa wajen yawaitar fyade”. A cewar Hajiya Gambo
A nata jawabin, Kwamishiniyar mata ta jihar Kano, Dr Zahra’u Muhammad ta ce,“ Al’umma su ci gaba da addu’a, domin Kano bama cikin matsala kamar yadda makwabtan jihohi su ke ciki, a yiwa shugabanni addu’a suma domin mu ji dadi, iyaye su kula da ‘ya’ya tare da addu’ar Allah ya bayar da damar yin tabiyar su”. Inji Dr. Zahra’u
Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron dinkI ya rawaito cewa, Hajiya Gambo ta kuma ja hankalin magidanta da su rinka taimakawa mata, su daina barin su dawainiyar gida su kadai.

Labarai
Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.
Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.
A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Labarai
Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.
Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.
“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.
Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.
Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Labarai
Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.
Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.
Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.
Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su