Connect with us

Labarai

Wani mai sana’ar Dankali ya kubuta dakyar a hannun dan damfara

Published

on

Wani matashi mai sana’ar Dankali dake unguwar Chiranci a karamar hukumar Kumbotso ya kubuta daga hannun wani mutum da ake zargin dan damfara ne yayi yunkurin karbe masa kudade.

Dan damfarar yazo wajen matashin ne da zummar sayen dankali sai kuma yaso karbar masa kudade ta hanyar hikimomi da ‘yan dabaru, kamar yadda ya shaidawa gidan rediyon Dala a ranar Talaya.

Ya na mai cewa, “Ina zaune a bakin titi ina bai wa mutane dankali, sai mutum ya turo yaro ya kira ni da na zo sai ya ce in zo da dankalin ya gani, da ya gani sai ya ce da yawa a ke so in dauko mu je, sai ya ce akwai dubu sha biyu a waje na? na ce a’a, sai na dauko dubu bakwai na bashi, sai ya ce, mu kai dankalin wani gida ni da yaron mu ce a ajiye wa Abba, naga alamun mutumin bashi da gaskiya, na dawo bakin titin na gan shi, mu ka bishi a kan mashin, na karbi kudi na. Na koyi darasi idan ban san mutum ba zan sake yarda da shi ba”. A cewar mai Dankali

Shima yaron da a ka aika ya kira mai dankalin ya ce, “Ni ban san shi ba, ya ce in zo a karbi dankali, shiyasa ma na gudu saboda ban shi ba, da tuni ya saka ni a wahala”. Inji yaron

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar, wani tela mai suna Mukhtar Ilyasu wanda al’amarin ya faru a kusa da shi ya ce, dan damfarar wajen say a fara zuwa kafin daga bisani yaje wajen mai sayar da dankalin.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending