Connect with us

Labarai

Marayu na bukatar tallafi a lokutan sallah – Dakta Auwal

Published

on

Gidauniyar tallafawa marayu da marasa karfi da ke garin Riga Fada a karamar hukumar Kumbotso mai suna Riga Fada Orphan and Less Privilege ta gabatar da taron bai wa marayu da marasa karfi kayan sallah.

Taron wanda ya gudana a garin Riga Fada a ranar Alhamis, daya daga cikin wadanda su ka samu tallafin a zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Ya ce, “Na gode a kan yadda kungiyar ta tallafa mana, kuma ina bukatar a siya min keken guragu, domin na samu saukin tafiya, cuta ce wadda ban dade da samun ta ba, an yi maganin amma abun ya faskara”.

Itama wata uwar marayu mai suna Hadiza Al Mustapha wacce ‘ya’yan ta su ka ci gajiyar tallafin, ta ce, “Mun yi farin ciki, Allah ya buda masu, ya kuma basu kwarin gwiwa, an baiwa ‘ya’yan mu yadiddiga a dinke”.

Kazalika, daya daga cikin jagororin kungiyar, Dakta Auwal Riga Fada ya ce, “Mun fahimci akwai yara da yawa da a ka mutu a ka bar su mata da maza, kuma ba su da wadanda za su dauki nauyin su, wadannan yaran idan sallah ta zo su na kaka. Shi yasa mu kaga dacewar mu samar musu kayan sallah da za su fito cikin farin ciki da na su kayan”.

Ya kuma ce, “Mawadata su tuna cewa, wata rana za su mutu, kuma ba su san yadda za su bar iyalan na su ba, don haka idan mutum ya taimaka to shima zai samu wadanda zasu taimaka masa”. A cewar Dakta Auwal

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, yara kimanani arba’in da kuma marasa makarfi biyar ne su ka ci gajiyar tallafin.

 

 

 

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending