Connect with us

Labarai

Ranar abota ta duniya: Mutum zai iya gyara rayuwar abokin sa – Malam Nuhu

Published

on

Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 30 ga watan Yulin ko wace shekara a matsayin ranar abota ta duniya, da nufin wayar da kai da kuma karfafa gwiwar zaman lafiya da farin ciki da kuma hadin kai a tsakanin al’umma.

Haka zalika abokai a sassa daban-daban na duniya kan aika sakonnin fatan alkairi ga abokan su da kuma musayar kyaututtuka na musamman a tsakanin su, tare da tabbatar da kyakkyawar alaka a tsakanin kabilu daban-daban ta hanyar abota.

Bikin ranar  kan mayar da hankali wajen ganin an sanya matasa a harkokin shugabanci ta hanyar karfafa alaka a tsakanin kabilu da kasashe daban-daban, ba tare da yin la’akari da yare ko kabila ko kasa ba.

Wani malami a sashen nazarin ilimin zamantakewar dan adam da ke jami’ar Bayero a nan Kano Dakta Aminu Sabo Dambazau, ya ce, “Akwai dalilai masu yawa da ke sanya mutane kulla alaka ta abota a tsakanin su da wasu”.

Ya kuma ce, “Abota ta na dorewa ne matukar akwai gaskiya da fahimtar juna da kuma taimakekeniya a tsakanin abokai, dabi’a ce ta dan adam ta bukatar wanda zai yi mu’amala da su, kasancewar babu wanda zai iya yin rayuwa shi kadai”. A cewar Dakta Aminu Sabo Dambazau

A na sa bangaren, wani malamin addinin musulunci Malam Nuhu Muhammad Tukuntawa, ya ce, “Abokai na tasiri sosai wajen gyara rayuwar abokan su idan a ka yi dacen samun abokai na gari”. Inji Malam Nuhu Muhammad

Malamin ya kuma yi kira ga iyaye da su rinka sanya ido kan irin abokan da ‘ya’yayen su ke mu’amula da su domin kaucewa yin alaka da gurbatattun abokai.

 

 

 

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending