AGOBE ASABAR NE ZA A GUDANAR DA ZABEN CIKE GURBIN DAN MAJALISAR DATTIJAI A JIHAR BAUCHI

Comments are closed

Kwamishinan ‘yansanda dake kula da ayukan zabe na shelkwatar ofishin ‘yansanda a Abuja, Ahmad Illiyasu, ya bukaci ‘yan siyasa dasu bada hadin kai ga jami’an tsaro domin gudanar da aikin zaben cike gurbi na dan majalisar dattijai da za’a yi gobe Asabar a jihar Bauchi.
Kwamishinan ‘yansandan, na wannan kiran ne yayin taron hadin gwiwa da jami’an tsaro da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta shirya domin gudanar da zaben cike gurbin.
Ahmad Illiyasu, bukaci ‘yan siyasa dasu bada hadin kai ga jami’an tsaron domin gudanar da aikin zaben cikin nasara.
Ya kuma ce ya zama wajibi ga duk wadanda suke da hannu a zaben dasu bi doka domin ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Shi kuwa a nasa jawabin jami’in hukumar zaben shiyar jihar Bauchi, Muhammad Yahaya, ya ce ma’aikatan zabe dubu uku ne zasu yi aikin zaben a rumfunar zabe dubu 1 da 900 a gobe Asabar.
Ya kara da cewar za a fara zaben ne da karfe takwas na safe har zuwa karfe hudu na yammacin Asabar.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close