AL’UMMAR UNGUWAR HOTORO SUN KOKA KAN YADDA HUKUMOMIN ILIMI SUKAYI WATSI DA TABARBAREWAR MAKARANTAR FIRAMAREN YANKIN

Comments are closed

Al’umar unguwar Hotoron Arewa a yankin karamar hukumar Nasarawa sun koka kan yadda hukumomin ilimi sukayi watsi da tabarbarewar yan aikin koyo da koyarwa a makarantar firamaren yankin.

Haka zalika, al’umomin sun bayyana damuwa kan yadda aikin gyaran titin unguwar ke tafiyar hawainiya tun bayan da gwamnati ta bada kwangilar gudanar da aikin.

A yayin ziyara ga dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa domin tunasar da hukumomin halin da suke ciki, shugaban tawagar al’ummomin Alhaji Muhammad Usman yace akwai bukatar mahukunta su kaimu su dauki domin ceto ilimin ‘yayan su daga durkushewa.

Da yake maida jawabi, wakilin Nasarawa a majalisar dokoki ta jihar Kano Alhaji Ibrahim Ahmad Gama yace “nan bada jimawa ba za’a fara aikin gudanar da garanbawul a makaranatar firamaren ta Hotoron arewa.”

Kansilan Hotoron Arewa, Alhaji Misbahu Auwal ya bayyana godiya a madadin al’umar yankinsa dangane da wannan mataki da gwamnati ta dauka akan batutuwan da suka koka akan su.

Wakilinmu Aminu Ahmad Abbas ya ruwaito cewa, ta kunshi dattawa da matasa da sauran masu ruwa da tsaki a yankin Hotoron arewa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close