AL’UMMAR GARIN GALINJA KAURAN MATA DAKE KARAMAR HUKUMAR MADOBI A NAN KANO SUN KOKA BISA HALIN KO’IN KULA DA GWAMNATOCI KE YI WAJEN SAMAR MUSU DA CIGABA A YANKIN SU

Comments are closed

Al’ummar garin Galinja Kauran mata dake karamar hukumar Madobi a nan Kano sun koka bisa halin ko’in kula da gwamnatoci ke yi wajen smara musuda cigaba a yankin su.
Shugaban tawagar gudanar da aikin gayya a kauyen na Galinja kauran mata, Malam Muhammad Sani ne ya bayyana hakan yayin kammala aikin gayya da suka gudanar tsahon kwanaki sakamakon lalacewar hanyar su.
Malam Muhammad Sani, ya kara da cewar, “mazauna garin na Galinja Kauran Mata, na fama da matsalar hanya yasa suke neman daukin wadanda ke da alhakin inganta rayuwar su.”
Su ma wasu cikin matasan da suka bayar da gudunmawar karfin su wajen gudanar da aikin gayyar sun bayyana kalubalen dake tattare da rashin hanyar musamman ma a lokacin damuna.
Kan wannan batun ne wakilin mu Abba Isah Muhamma ya yi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar Madobi Malam Lawan Yahaya, ta wayar tarho bai same shi ba, ya kuma tura masa sakon karta kwana amma har yanzu bai amsa ba.
Wakilin namu ya kuma rawaito cewa, mazauna garin na Galinja Kauran Mata, na fatyan gwamnati za ta dauki matakin ceto rayuwar su ta fannin ababen more rayuwa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close