AN BAYYANA CEWA BABU WANI ALKALI DA YAKE YANKE HUKUNCI AKAN LAIFI HAR SAI YA GA LAIFIN A RUBUCE

Comments are closed

Kakakin rukunin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya bayyana cewa babu wani alkali da yake yiwa wanda ake tuhuma hukunci akan kowanne irin laifi har sai ya ga laifin a rubuce.
Baba Jibo ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala a yau.

Ya ce bayan korafe-korafen da ake yi dangane da zargin yansanda suna gurfanar da masu laifi a kotu wadanda an daina yayin su har sai an rubuta a rubuce.

Ya kuma ce akwai ranakun da doka ta tanada dan sadar da mutum ga sammaci. Baba Jibo Ibrahim ya kara da cewa akwai muhimman dalilan da suke tasowa akai wa mutum sammace, ba sai ranar da doka ta tanada ba.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close