AN BUKACI DALIBAN DA SUKA KAMMALA KARATU DA SU RINKA DUBA IRIN MATSALOLIN DA TSAFFIN MAKARANTUNSU KE FUSKANTA

Comments are closed

An bukaci daliban da suka kammala karatu da su rinka duba irin matsalolin da tsaffin makarantunsu ke fuskanta, tare da tallafawa makarantun domin cigaban harkokin ilimi a jihar kano dama kasa baki daya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar tsofaffin dalibai na kwalejin fasaha ta Polytechnic dake nan kano sashen koyar da na’ura mai kwakwalwa ya fitar, yayin taron shekara-shekara da kungiyar ta gudanar anan kano.
Sanarwar ta ambata cewa, shugaban kungiyar Lurwanu Yusif Dausayi da sakaren ta Aminu Adam kibiya, suna yabawa wasu daga cikin jiga-jigan malaman kwalejin, da suka hadar da Malam kabiru Dalha kabir, da kuma Malam Hussaini Jibril bisa irin gudunmawar da suke bayarwa a harkokin ilimi a kwalejin.
Sanarwar ta kuma bukaci ‘ya’yan kungiyar da dasu kasance tsintsiya madaurinki daya, domin tallafawa kwalejin ta Polytechnic, dama harkokin ilimi a fadin jihar kano.
Sani Magaji Garko ya kuma ce a yayin taron, kungiyar ta sake gudanar da sauye-sauyen shugabancin kungiyar, tare da duba yadda za’ayi mata rijista domin kawo cigaban da ake da bukata.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close