AN CE BINCIKEN DA AKE GUDANARWA A KAN BATUN FAIFEN BIDIYON GWAMNAN KANO YA NA NAN DARAM

Comments are closed

Kwamitin zauren majalisar dokokin jihar Kano da yake binciken hoton faifen bidiyon da ake zargin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, da karbar daloli a hannun ‘yan kwangila, ya ce binciken da yake gudanarwa a kan batun faifen bidiyon ya na nan daram.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jiha, kuma shugaban kwamatin binciken hoton faifan bidiyon, Dr Baffa Babba Dan Agundi ne ya tabbatar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin jiya.
Ya ce a matsayin su na masu yin doka, za su cigaba da gudanar da aikin su na kwamiti kan hoton faifain bidiyon.

Ya kuma ce kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa ‘yan majalisun dokokin jihohi kasar nan, damar gudanar da bincike a ko wane irin mataki.

Wakiliyar mu a zauren majalisa, Khadija Ishaq Muhammad, ta rawaito mana cewa, kwamatin binciken hoton faifan bidiyon zai cigabada da gudanar da binciken hoton faifan bidiyon tare da kwararru masana harkar hoto mai motsi don tabbatar da sahihancin ingancin bidiyon.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close