AN CE MAJALISAR DOKOKIN KANO BA TA DA KAYAN AIKIN YIN CIKAKKEN BINCIKE GAME DA ZARGIN CIN HANCI DA AKE WA GWAMNAN JIHAR

Comments are closed

Shugaban kwamitin shugaban kasa a kan yaki da cin hanci, Farfesa Itse Sagay, ya ce majalisar dokokin Kano ba ta da kayan aikin da za ta iya yin cikakken bincike a kan badakalar cin hanci da ake zargin gwamna Abdullahi Ganduje ya na yi a wasu faifan bidiyo dake yawo a kafafen sadarwa na zamani.
Da yake tattaunawa da jaridar Leadership, a ranar Talata, Sagay ya ce bincike a kan bidiyon na bukatar kayan aiki na musamman abin da majalisar dokokin jihar Kano ba ta da karfi da kuma fasahar gudanarwa.
Ya ce a kashin kansa zai so ya ga daya daga cikin ‘yan kwangilar ya fito ya ce, lallai shi ne ya baiwa gwamnan daloli, kuma ya na sauraron faruwar hakan, in kuma maganar binciken gamnan ne, to ai, a kwai hukumomi da aka kafa don irin wannna ayyukan, kamar su EFCC da sauransu.
Ya ce bai fahinci dalilin da majalsisar dokokin Kano ta jefa kanta a kan wannan badakalar ba, don kuwa a bayyane lamarin yake cewa, basu da kayan aikin gudanar da bincike a kan bidiyon yadda ya kamata, lallai a halin yanzu a kwai rudani a kan lamarin, a halin yanzu bazan iya cewa, komai ba har saai na asamun tabbacin an aikata laifi kafin ya san yadda za a fuskanci lamarin gaba daya.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close