AN KAMMALA TARON KUNGIYAR LAUYOYI MUSULMI NA YINI UKU DAYA GUDANA A NAN JIHAR KANO

Comments are closed

A jiya lahadi ne aka kammala taron kasa na yini uku da kungiyar lauyoyi musulmai wato MULAN a takaice ta shirya a nan Kano.

A yayin taron wadda ‘yayan kungiyar daga sasa daban daban na kasar nan sukahalarta, angabatar da kasidu daga masana a fannoni da damanarayuwa.

Taron na bana wadda shine karona 11, ya maida hankali ne akan batutuwan da suka shafi tsaron kasa, da ‘yancin bil’adama kana da kuma al’amuran ci gabaan rayuwar ‘yankasa.

Tsohon kwamishinan shari’a na jihar Kano Barrister Aliyu Umar SAN wanda shine shugaban kwamitin shirya taron ya yi karin haske dangane da makasudun kafa kungiyar lauyoyi musulmai a najeriya.

Shugaban kungiyar lauyoyi musulmai ta kasa reshen jihar Kano Barrister Ibrahim yace “ayyukan kungiyar baida kaita ga al’umar musulmi bakawai.”

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwato cewa, a karshen taron kungiyar na bana an fitar da takardar bayanin taron maikunshe da shawarwari ga gwamnati hukumomin tsaro, alkalai da lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki game da matakan inganta rayuwar ‘yan kasa musamman ta fuskar tabbatar da adalci a tsakanin ‘yankasa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close