AN KARRAMA BATUREN ‘YANSANDAN DAWAKIN TOFA BISA KOKARIN DA SUKAYI NA DAKILE YUNKURIN DAUKE WANI MUTUM DA MASU GARKUWA DA MUTANE SUKA YI

Comments are closed

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta karrama baturen ‘yansandan dawakin Tofa SP Ahmad Hamza, bisa namijin kokarin da jami’an sa sukayi na dakile yunkurin dauke wani mutum da masu garkuwa da mutane sukayi.
Kakakin rundunar a nan Kano SP Magaji Musa Majiya, ya bayana cewar a ranar 3 ga watan da ya gabata ne, wasu da ba’a San ko suwaye ba, suka yi yunkurin yin garkuwa da wani mutum a yankin, amma sakamakon rahoton gaggawa da baturen ‘yansandan ya samu suka kai dauki tare da fatattakarsu.
SP Majiya, ya kara da cewar Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, Malam Rabiu Yusif, ya bullo da tsarin yabawa ‘yansandan ne don karfafamusu gwiwa wajen gudanar da aiki bisa kwarewa.

A nasa jawabin baturen ‘yansandan na Karamar hukumar ta Dawakin Tofa, SP Ahmad Hamza, ya bayana cewar lambar yabon zata karfafa masa gwiwa wajen cigaba da aikin tsaron rayuka da dukiyar alumma kamar yadda tsarin aikin na dansanda ya tanadar.

Wakilin Mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar hukumar na gargadin Jam’anta da su rinka gudanar da aiki bisa tsarin doka, tare da neman Karin bayanan sirri daga Jama’ar gari don kara inganta harkokin tsaro a fadin jihar Kano.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close