GWAMNATIN JIHAR NEJA TA KAI ZIYARA KAUYEN RAFINGORA.

Comments are closed

Gwamnatin jihar Naija ta kai ziyara kauyen Rafingora dake karamar Hukumar Kontagora a jihar, sakamakon anbaliyar ruwa da ta faru a yankin wanda yayi sanaddiyar mutuwa mutane 10 tare da rushe gidaje sama da 300.

A makon da ya gabata ne dai Hukumonin jihar Naija suka tabbatar da mutuwar wasu matasa 10 tara da yin awon gaba da gidajen jama’a kimanin 300 a kauyen Rafingora dake karamar Hukumar kontagora.

Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce, “har yanzu mutanen garin na cikin hadari bisa la’akari da abinda ya gani, don haka zasu nemi tallafin gwamnatin tarayya domin tabbatar da an canza wa mutanen garin matsugunni.”

Gwamnan ya kara da cewa, “mazaunan garin suna cikin wani yanayi na tashin hankali a sakamakon hasarar matsugunan su da kayayyakin abinci, a don haka suka dauki gabaren sauyawa wadanda suka rage matsuguni don gudun kada anbaliyar ruwan ta shafe su.”

A halin yanzu Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar na ci gaba da tattara bayanai domin tantance asarar da ambaliyar ruwan ta haddasa kamar yadda shugaban hukumar Alhaji Ibrahim Inga ya tabbatar.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close