HUKUMAR DUBA LAFIYAR ABABAN HAWA A NAN KANO TA AYYANA MASU ARON HANNU A MATSAYIN MASU LALURAR TABIN KWAKWALWA

Comments are closed

Hukumar duba lafiyar ababan hawa a nan Kano BIO, ta ayyana masu aron hannu wato one way a matsayin masu lalurar tabin kwakwalwa.
Manajan Daraktan hukumar a nan Kano, Alhaji Garba Gaya ya bayyana hakan a lokacinda ya ke ganawa da manema labarai a wani taro da aka gabatar da ofishin mai bai gwamnan Kano shawara a kan ababan hawa ya shirya na horar da direbobi.
yace mai tukin abun hawa kamar mota, babur da makamantansu da ya ke bin hannun da ba nasa ba to yana cikin hadari, kuma ganganci ne da kasada da ka iya jawo asarar rai da dukiya da sauransu wanda mai cikakken hankali ba zai iya yin gangancin jefa rayuwarsa da ta al’umma cikin hadari ba.
Ya kuma ce bin hannun da ba naka ba a lokacin tuki masuyin hakan, ba mamaki in an auna kwakwalwarsu a samu suna da tabin hankali don haka mutane su guji karya dokar tuki don kare lafiyar sa da ta al’umma.
Haka zalika ya kuma bayyana takaicinsa a kan yadda har yanzu lasisin tuki na bogi yake da yawa a tsakanin masu tuki, bisa kiyasi duk da ba wata kididdiga da za a ce ga adadin su ba, amma dai har yanzu marasa lasisin tuki sunfi masu lasisin tuki yawa a kasar nan.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close