PRAMINISTAN BIRTANIYA ZATA FARA RANGADI A NAHIYAR AFRIKA

Comments are closed

A karon farko tun bayan zamowa firai minister Birtaniya a shekarar 2016, Theresa May za ta ziyarci nahiyar Afrika.
Misis May za ta fara ziyartar Afrika ta Kudu ne a gobe Talata kafin ta iso Najeriya sannan ta je da Kenya, a cikin shirinta na bunkasa ciniki da nahiyar bayan Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai.
Ta ce wannan tafiyar za ta kasance wata babbar dama a lokaci mai cike da tarihi ga Britaniya.
Ta kuma ce tana son bunkasawa da kuma karfafa dangantakar Britaniyar da wasu sassa na duniya gabanin ficewar kasar daga Tarayyar Turai.
‘Yan kasuwa 29 za su raka Misis May zuwa wadannan kasashen uku.
Ana kuma sa ran za ta tattauna a kan batun tsaro bayan ta iso Najeriya musamman rikicin Boko Haram da rawar da sojojin Britaniya da aka girke a Kenya ke takawa wajen yaki da mayakan al Shabab a Somaliya.
A ranar Laraba za ta isa Abuja domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, kafin ta wuce zuwa birnin Legas.
Kakakin ofishin firai minister da ke Downing Street ya ce wannan ziyarar na da zummar karfafa tsaro da inganta zaman a Afrika ne domin kasashen nahiyar na fuskantar kalubalen tsaro da na siyasa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close