SHUGABAN LIMAMAN DARIKAR KADIRIYYA YA YI KIRA GA AL’UMMA MUSAMMAN DA SU RINKA TAIMAKAWA HARKOKIN ADDININ MUSULUNCI

Comments are closed

Shugaban limaman darikar kadiriyya Malam Bazallahi sheik Nasir Kabara, ya yi kira ga Al’umma musammam mawada da su rinka taimakawa harkokin addinin musulunci, domin samun lada a gobe kiyama.
Malam Bazallahi ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’ar da ta gabata a yayin taron bude wani masallacin Juma’a na wucin gadi a garin Lambu dake karamar hukumar Tofa anan kano.
Yace ta haka ne za a sami duk wata nasara da ake so a samu dan cigaban addinin musulunci.
Shi ma guda daga cikin limaman masallacin Juma’ar dake garin Lambu malam Muhammad Muktar Musa, godiya ya yi ga Al… bisa samun nasarar da aka yi dangane da bude masallacin bayan daukar tsahon lokaci da aka yi anasa ran budewa.
Malam Muktar ya kuma kara da cewa batun dadewa da masallacin ya yi ba tare da an kammala shi ba kaddara ce, kuma abu ne dake bukatar dogon bayani.
Wakilin mu Abuabakar sabo ya rawaito cewa an kwashe shekaru 18 ana gina masallacin na garin Lambu kuma har kawo yanzu ba akai ga kammala shi ba, lamarin da yasa al’ummar yankin suka sami wani a matsayin na wucin gadi.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close