SHUGABAN MAJALISAR DATTIJAI YA CE DOKOKIN KASA SUN FAYYACE KA’IDOJI DA HANYOYIN TSIGE SHUGABAN MAJALISA DATTAWAN KASAR NAN

Comments are closed

Shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya ce dokokin kasa sun fayyace ka’idoji da hanyoyin tsige shugaban majalisa dattawan kasar nan.
Ya ce ‘tsarin dokokin majalisar yayi tanadin cewa sai an samu kashi biyu bisa uku na yawan mambobin majalisar kafin a kai ga tsige shugaban.”
Sanata Bukola Saraki wanda ke wadannan kalamai lokacin taron manema labarai a Abuja, ya ce ba shi da muradin dawwama akan kujerar shugabancin majalisar bisa yanayi na ko a mutu ko ayi rai ba.
Sun ce basu amince da shi ba a matsayin shugaban majalisar to babu makawa zai iya barin kujerar sa.
Shugaban majalisar dattawan, wanda ya zargi hukumomin tsaro da kokarin cin zarafi ga tsarin demokradiyar Nijeriya, yay aba da matakin da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya dauka na sallamar shugaban hukumar tsaro ta DSS.
Sai dai Sanata Bukola Saraki, ya bukaci bangaren zartarwa na gwamnati ya cigaba da irin daukar irin wadannan matakai akan duk wani jami’in tsaro dake kokarin kawo tarnaki da tsarin demokradiyar Nijeriya.
Ya kara da cewar, a bangaren ta majalisar dokoki ta kasa za ta cigaba da yin dukan mai yuwa domin kare mutunci da kimmar Nijeriya a idon duniya ta hanyar gudanar da ayukan ta bisa tanadin dokokin kasa domin wanzar da demokradiya da cigaban al’ummar kasa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close