WANDA AKE ZARGIN DA DAUKAN HOTON BIDIYON GWAMNAN KANO YA CE ZAI BAYYANA A GABAN KWAMITIN DA KE BINCIKEN AL’AMAMARIN IDAN GWAMNAN MA ZAI ZO

Comments are closed

Mutumin da ake zargin ya dauki hoton bidiyon dake nuna gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar daloli daga hannun’yan kwangila, ya ce zai bayyana a gaban kwamitin dake bunciken al’amarin matukar shima Gandujen zai zo da kansa ba sakoba.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata wasika da lauyan mai fallasar, Barista Sa’idu Muhammad Tudun Wada, ya aikewa da kwamitin na majalissar dokoki, yana mai cewa, a yayin zaman a gayyaci masana harkar hoto mai motsi daga hukumar S.S da kuma wani masanin daga kasar waje da kuma Jafar-Jafar sai kuma sheik Aminu Ibrahim daurawa.
Lauyan mai fallasar ya kuma ce, a yayin zaman a kawo dukanin faya-fayan bidiyon, harma da wadanda ba a saki ba, shi kuma zai kawo dukkanin muhimman abubuwan daya ya yi amfani dasu wajen daukar bidiyon, ciki harda kyamarar, tare da bada damar ayi masa tambaya daga daya zuwa goma, wadanda za’a mika masa su, kafin ya bayyana a gaban kwamitin.
Karin wani sharadin da lauyan mai fallasar ya bayar shi ne, wanda yake tsayawa zai yi badda bami fuska tare da boye sunansa, kuma zaman ya kasance da karancin mutane da kuma samun kariya daga hukumomi tsaro don kare rayuwarsa data iyalansa da kuma kasuwancinsa.
Acewar lauyan mai fallasar Sa’idu Muhammad Tudun Wada, Wanda yake tsayawa ya kuma bukaci da ya mika kwafin wasikar ga hukumomin, I.C.P.C da shugabannin kungiyoyin lauyoyi na kasa data ‘yan jaridu, sai kuma kungiyar Amnesty mai kare hakkin dan adam da tabbatar da daidaito a ayyukan gwamnati da hukumomi, sai kuma ta karshe kungiya mai tabbatar da hakokin zamantakewa dana tattalin arziki da bin diddigi.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close