WASU ‘YAN MAJALISUN DOKOKIN JIHAR KANO SU SHIDA SUN SAUYA SHEKA DAGA JAM’IYAR APC ZUWA PDP

Comments are closed

Wasu ‘yan majalisun dokokin jihar Kano su shida sun sauya sheka daga jam’iyar APC zuwa PDP.
Shugaban majalisar dokokin jiha, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ne ya karanto wasikar sauya shekar yayin zaman majalisar da ya gudana a yau Laraba.
Ya ce a cikin ‘yan majalisun da suka sauya shekar zuwa jam’iyar PDP, akwai mai wakiltar karamar hukumar Gwale, Yusuf Babangida Sulaiman da Rabi’u Saleh daga Gwarzo da Zubairu Mahmud daga Madobi da Yusuf Abdullahi Falgore daga Rogo da Hamza Sule Bichi mai wakiltar Bichi sai kuma Isyaku Ali Danja daga Gezawa.
Ya zuwa yanzu jam’iyar PDP na da mambobi 7 a cikin ‘yan majalisu 40 na majalisar mambobin dokokin jihar Kano.
A jiya Talata ne dai tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya koma jam’iyar PDP tare da wasu mukaraban sa 10.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close