WATA KUNGIYA A KARAMAR HUKUMAR TARAUNI TAYI KIRA GA KUNGIYOYIN DA DA-DAITUN MUTANE SU RINKA TAIMAKAWA MARAYU

Comments are closed

Wata kungiya mai rajin tallafawa marayu da masu karamin karfi da ke Unguwa uku a karamar hukumar Tarauni, tayi kira ga kungiyoyi da dai-daikun mutane su rinka taimakawa marayu.
Shugaban kungiyar Abdulbasir Yakubu Khalil, ne yayi wannan kiran yayin gudanar da wasu wasanni da kungiyar ta shiryawa marayu a ofishin hukumar Hisba da ke unguwa uku a karshen makon nan.
Abdulbasir ya ce ta hanyar tallafawa marayu ne za`a samar da ingantacciyar alumma tare da tattalin arziki mai dorewa.
Suma wasu daga cikin Marayu da masu karamin karfi da suka halarci wasannin sun bayyana jindadin su.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewar, a yayin wasan an gudanar da wasan tseren buhu da wasan kwaikwayo, kuma wannan shi ne karo na 5 da kungiyar ke shiryawa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close