A DAI NA HAWAN JEMAGE A ADAIDAITA SAWU

Comments are closed

Shugaban Kungiyar matuka babur masu kafa uku wato babur din adaidata sahu, wanda aka fi sani da TOAKAN na nan jihar Kano, Sani Sa’idu Dankoli, ya ce kungiyar ba ta yarda da zaman gefan da wasu matuka babur din ke yi wanda ake kira da hawan jemage.

Sani Sa’idu Dankoli, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala.

Ya ce ”kungiyar ta haramta hawan gefan da wasu matuka babur din ke yi da kuma saka kayan da basu dace bag a matuka baburan.

Ya kuma ce ”a don hakane kungiyar ta shigar da korafin ta ga hukumomin tsaro don daukar mataki”.

Shugaban kungiyar, Sani Sa’idu Dankoli, ya kuma yi kira ga duk wani matukin babur din Adaidaita sawun da su kiyaye wajen bin dokokin kungiyar in kuma ba haka ba dole ne kungiyar ta dauki matakin ladabtarwa ga duk wanda aka kama da karya doka.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close