A YI BIKIN TAKUTAHA CIKIN LAFIYA

Comments are closed

Shugaban kungiyar sha’irai ta kasa Sharif Rabi’u Usman Baba yayi kira ga daukakin sha’irai da sufita Bikin takuta cikin kwanciyar hankali da lumana dan gujewa tashin tashina da rigimar magoya baya dan kiyaye bacin ran wani.

Sheriff rabiu baba Yayi wannan kiran ne yayin zantawar su da wakilin gidan radion dala a gidan sa dake janbulo

Ya ce”ya kamata hukuma ta kara tsaurara tsaro domin tabbatar da anyi zagayan takutahan a cikin kwanciyar hankali da lumana wanda zaayi a kwaryar birnin kano da kewaye”.

Rabi’u Usman Baban ya kara da cewa hakika wannan rana ta takutaha rana ce ta farin ciki ga dukan musulmai shi yasa ma sukan fito kwansu da kwarkwata  dan nuna farin cikin su da ranar.

Wakilin namu Nura Ahmad Hassan ya rawato cewa Dr. Siwidi Muhammad Hassan yace anfara  bikin Takutaha ne a Shekara Dari tara da 14 bayan Hijjirar wacce tayi dai dai da Shekara ta Dubu daya da dari biyar da 65 miladiya.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close