A ZABI SHUGABANNI MASU KISHIN ILIMI DA LAFIYA INJI SEDSAC

Comments are closed

Kungiyar bunkasa ilimi da daidato da zamantakewa da kuma bunkasa demokradiya, SEDSAC, ta bukaci al’ummar kasar nan ka da su zabi duk wani dan takarar gwamna ko shugaban kasa a zaben 2019, har idan bai mayar da kai wajen bunkasa harkokin ilimi da bangaren lafiya.

Kungiyar SEDSAC, ta bukaci hakan ne a cikin wata takardar kungiyar mai kunshe da sa hannun mataimakin daraktan kungiyar na musamman, Kwamrade Habibu Dahiru Sagagi, da ya rabawa manema labarai.

Kungiyar ta ce fannin ilimi da lafiya na da matukar amfani ga rayuwar al’ummar kasar nan, amma yawancin shugabannin kasar nan na yin shakulatin bangaro da  fannin ilimi da lafiya.

SEDSAC, ta kara da cewar, majalisar dinkin duniya ta bukaci kasar nan da ta rinka saka kaso 26 da kuma 21 a dukannin bangarorin na fannin ilimi da lafiya a kowane kunshin kasafin kasar nan.

Haka zalika, kungiyar ta kuma yi kira ga shugabanni da su guji yin kalamin kiyaya yayin gangamin yakin neman zaben don guje tunzira magoya bayan su.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close