AN BUKACI IYAYE DA SU RINKA KAI ZIYARA MAKARANTUN ‘YA’YAN SU

Comments are closed

Daraktan Makarantar Abubakar sadiq Islamiyya da ke Ja`en a karamar hukumar Gwale dake nan kano, Malam Kabiru Muhammad ya bukaci iyayen yara da su rinka ziyartar makarantun yayansu don ganin halin da makarantun ke ciki.

Malam Kabiru Muhammad ya bayyana hakan ne yayin bikin Saukar karatun Alqurani mai Girma na makarantar Abubakar saddiq, Wanda ya gudana a karshen makon daya gabata.

Yace ”ta hanyar kai ziyara makarantun ne kadai za`a iya samar da ingantaccen ilimi ga yaran su”.

A nasa jawabin shugaban makarantar Malam Sunusi Sani Adam, Jan hankali yayi ga  matasa da su tashi tsaye wajen Neman ilimin addini da na zamani domin samin gwaggwabar rayuwa.

Wasu daga cikin daliban sun bayyana farin cikinsu bisa saukar da sukayi, tare da fatan cigaba da bitar abinda suka koya ba tare da sunyi watsi da karatun nasu ba.

Wakilin mu Ahmad Rabiu Ja`en ya rawaito cewa Dalibai 22 ne suka kammala saukar karatun ciki akwai maza 7 mata 15.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close