AN GURFANAR DA WASU YAN KASUWA A GABAN KOTU

Comments are closed

Wasu matasa da su ke kasuwanci a kantin kwari, an gurfanar da su a gaban kotu bisa zarginsu da yin sojan gona.

Matasan da ake zargin an gurfanar da su ne a gaban kotun shari’ar musulunci da ke zaman ta a Kurna, karkashin mai shari’a Nasir Abba Magashi.

Wani daga cikin ‘yan kasuwar ta kantin kwari ne mai suna Sadi Sa’idu, ya gurfanar da wadanda ake zargin agaban kotu, wadanda suka hada da, Sharhabilu, da Dankani da Jamilu da Alhaji Bala yalwa, sai kuma shugaban kungiyar ‘yan teburan kantin kwari Alhaji Aminu Kawu, kamar yadda Dan’uwan mai kara Rabiu Sa’id ya bayyana.

Shima lauyan mai kara Barista Saleh Idris Bello y ace ”sun a nan akan batun sulhu, in har kuma baiyi ba zasu cigaba da shari’a”.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa wadanda ake zargin sun amsa tuhumar da ake musu, an kuma dage zaman kotun zuwa ranar 3 ga watan Disamba domin cigaba da shari’a.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close