DAGACI YA JA KUNNEN IYAYE KAN KARATU

Comments are closed

Dagacin sheka Alhaji Musa Zakari yayi kira ga iyayen yara da su rinka tallafawa malaman makarantun Islamiyya domin tafikar da harkoki da kuma samar da ingantaccen ilimin addinin musulunci ga ‘ya’yan su.

Alhaji Musa Zakari ya bayyana hakan ne yayin bikin saukar alqur’ani mai girma na Makarantar Darussalafiyya wal Tahfeezul qur’an Da ke sheka sabuwar Abuja.

Ya ce ”duba da cewa iyaye su ne ke da alhakin baiwa yayan su ilimi, adon haka wajibi ne iyaye su rinka tallafawa malaman makarantun islamiyyun wajen tafikar da harkokin su”.

A nasa jawabin shugaban hukumar zabe ta jihar kano Farfesa Ibrahim Garba Sheka kira yayi ga al’umma da su kara tallafawa makarantun islamiyyu.

Da ya ke jawabin shugaban makarantar Mallam Salisu Abubakar Musa yabawa kungiyar iyaye da malaman makarantar yayi tare da kira da a tallafa musu wajen ginin makarantar.

Wakilin mu Abdullahi Aliyu Dangoro ya rawaito cewa Dalibai 132 sukayi saukar, ciki akwai maza 35 mata 97.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close