DAGACI YACE IYAYE SU RINKA KULA DA ‘YA’YAN SU KAN BANGAR SIYASA

Comments are closed

Dagacin Dorayi Babba Alhaji Badamasi Bello ya bayyana cewa samun cikakkiyar kulawa ga iyaye yana bada gaggarumar gudunmawa wajen hana yara matasa shiga cikin bangar siyasa da shan miyagun kwayoyi.

Alhaji Badamasi ya bayyana hakan ne yayin saukar alqur’ani mai girma na makarantar Ibqa’ul Hizburrahim islamiyya karo na tara, wanda ya gudana a asabar din data gabata.

Ya ce ”duba da yadda matasa ke fadawa cikin harkar bangar siyasa da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi akwai bukatar iyayen sukara saka idanu akan ‘ya’yan su”.

Shugaban makarantar Malam Mustafa Abubakar Samajidu ya bayyana kalubalen da makarantar ke fuskanta.

Wakilin mu Munzali Aliyu Yamadawa ya rawaito cewa Dalibai 36 ne su ka yi saukar, ciki akwai maza 9 mata 27.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close