MATASA SU GUJI SHIGA BANGAR SIYASA

Comments are closed

Mai unguwar yamadawa dake karamar hukumar Gwale anan kano Alhaji Ahmad Badamasi Bello, ya ja hankalin matasa da su zage damtse wajen hidimtawa harkokin addini.

Alhaji Ahmad Badamasi, ya bayyana hakan ne yayin mauludin Annabi SAW da ya gudana a unguwar Yamadawa a jiya Litinin.

Ya ce ”sai da hidimtawa addini ne za’a gane mutum yana kaunar Annabi SAW a ayyukan sa”.

Ya kuma ja hankalin matasa da su guji shiga bangar siyasa musamman a wannan lokaci da ake gudanar da yakin neman zabe.

Wakilin mu Munzali Aliyu Yamadawa ya rawaito cewa a yayin bikin mauludin an karrama wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar da suke bada gudunmawa, ciki kuwa har da Aliyu wali na nan gidan rediyon Dala.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close