TAIMAKO MATASA ITA CE HANYAR BUDIN MATASA

Comments are closed

Shugaban kwamitin Ilimi na Gidauniyar Al`huda foundation dake unguwar dorayi karama dorawar malam, Dahiru Nuhu ya bayyyana taimakekeniya sana’o’in hannu a tsakanin matasa a matsayin hanyar magance rashin aikin yi ta hanyar koyar dasu sana’o’in hannu maimakon jiran aikin gwamnati.

Malam Dahiru Nuhu, ya bayyana hakan ne yayin taron hada kan matasan yankin na dorayi wanda ya gudana a karshen mako.

Ya ce idan har aka bar matasa kara zube babu sana`a, zai iya haifar da ‘da mara ido , duba da muhimmancin matasa da cigaban kowacce alumma.

Wasu daga cikin matasan da suka halarci taron sun bayyana irin gudunmawar da zasu bayar ga yan uwansu matasa ta fannin sana’o’in da suka iya na hannu.

Wakilinmu Abba Isa Muhd ya rawaito cewa, an kuma ja hankalin alumma wajen jan matasa ajiki tare da tallafawa hazikan cikinsu ta bangaren karatu da sana`a.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close