‘YAN SIYASA KADA KU HALLAKA MATASA A ZABE

Comments are closed

Shugaban Kungiyar hada kan jam’iyyun siyasa don samar da zaman lafiya, Muhammad Abdullahi Raji, ya gargadi ‘yan siyasa da su gudanar da yakin neman zabe ba tare da jagaliya da dabanci ba, don kaucewa jefa rayuwar matasa cikin halaka.

Muhammad Raji ya bayyana hakan ne ta cikin shirin shari’a a aikace da ya gudana da safiyar yau a nan gidan rediyon Dala.

Ya ce ”kiyaye doka shi ne matakin farko ga kowane Dansiyas, matukar yana bukatar cikakkiyar Demokradiyya, sai dai idan hakan ta faskara zasu dauki mataki”.

Ya kuma kara da cewa ”kamata yayi matasa su kauracewa biyewa batagarin ‘yan siyasa”.

Muhammad Abdullahi Raji ya kuma bukaci iyaye da sauran al’umma da su bada tasu gudunmawar, wajen kula da ‘ya’yayen su tare da hada hannu da Jami’an tsaro don dakile matsalar musamman a wannan lokaci da aka fara yakin neman zabe.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close