ZA A DAU NAUYIN KARATUN DALIBI HAR YA KAMMALA KARATU

Comments are closed

Kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Bayero aji na shekarar 1992, bangaren ilimin dokokin Kasuwanci, sun kudiri niyar tallafawa daliban da suka sami sakamako mai kyau a jarabawar karshe.Shugaban kwamatin tsare-tsaren kungiyar, ACP Naziru Bello Kankarofi wanda shine mataimakin kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, ya tabbatarwa da hakan a zantawarsa da gidam Rediyon Dala.

Ya ce daga yanzu duk dalibin da ya taka muhimmiyar rawa a bangaren karatun sa na Business Law zai sami tagomashi daga kungiyar.

Ya kara da cewa, duba da yanayin da ake ciki suka ga dacewar tallafawa masu karamin karfi ta hanyar kai gudunmawa asibitoci da ma fitar da masu kananan laifi daga gidan Yari.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa ACP Naziru Bello Kankarofi, ya kuma shawarci sauran kungiyoyi tare da daidaikun al’umma da su rinka tallafawa hazikan dalibai don cimma burin su.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close