ZAUREN LAUYOYI NA TAHIR CHAMBERS TA BUKACI MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO DA TA BINCIKI GWAMNAN KANO KAN FITO DA KANANAN YARA KAN TITI

Comments are closed

Zauren lauyoyi na Tahir Chambers ta bukaci majalisar dokokin jihar Kano da ta binciki gwamnan kano Dakta Abdallahi Umar Ganduje da gwamnatin sa,kan fito da kananan yara yan firamare da akayi a kan titi suna daga kwalayen nuna goyon bayan gwamna kan zargin karbar kudaden daloli a hannun yan kwangila.
Cikin wata takarda mai kunshe da sa hannun shugaban zauren, Dahiru Ibrahim, ta ce fito da yara yan firamare kan titi da sunan goyon baya a lokacin da titinan suke cike da magoya bayan ‘yan siyasa daban-daban, barazana ne ga rayuwar su kuma keta haddi ne da cin zarafin kananan yaran.

Sanarwar ta kuma ce lokacin da aka fito da yaran lokaci ne da ya kamata ace yaran suna aji suna daukar Darasi, amma sai aka fito da su, dauke da kwalaye na nuna goyon bayan gwamnan , wanda hakan cin mutuncin ofishin gwamna ne.

Ta cikin sanarwar, ya bukaci majalisar da ta gaggauta matakin bincikar gwamnan bisa la’akari da dokar hakin kananan yara ta majalisar Dinkin Duniya da kuma ta gamayyar kungiyoyin kasashen Afrika da kuma kundin tsarin mulkin kasar nan don kaucewa jefa rayuwar kananan yara cikin halaka.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close