Gwamnatin Kano ta musanta janye motocin ɗaukar ɗaliban makarantun Sakandire mata daga aiki a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta ce ƙarancin motocin ɗaukar ɗalibai mata ƴan makarantun Sakandire da ake fuskanta, na da alaƙa ne da gyaran wasu daga cikin motocin da ake yi, saɓanin yadda wasu ke yaɗawa cewar an ɗauke su daga gudanar da aiki a sassan jihar.
Kwamishinan Ma'aikatar Ilimi Gwani Dr. Ali Haruna Makoɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da wasu daga cikin ɗalibai ƴan mata na makarantun Sakandire ke yi kan yadda suke fuskantar ƙarancin motocin ɗaukar ɗalibai da gwamnatin domin kai su makaranta da mayar da su.
Da yake jawabi a madadin Kwamishinan, Babban Sakatare a Ma'aikatar ilimi ta jihar Kano, Bashir Baffa Muhammad, ya ce ƙarancin motocin da ɗaliban suke fuskanta na da alaƙa ne da gyare-gyaren da ake yi a wasu daga cikin motocin, domin ƙara sauƙaƙa wa ɗaliban a karatun su.
Ya kuma ce nan gaba kaɗan za a ƙara wadata motocin a sassan jihar Kano, da zarar an kammala gyaran waɗanda suka samu matsala, domin ci gaba da taimaka wa karatun ɗalibai a faɗin jihar.
A cewar sa, "Ba janye motocin aka yi ba domin ko a yanzu akwai waɗanda suke aiki, suma waɗanda suka samu matsala da kaɗan da kaɗan ake gyara su, da zarar an kammala gwamna Abba Kabir Yusuf, zai ƙaddamar da su, su dawo aiki," in ji shi.
Wakilinmu Adam Abubakar Indallahi ya ruwaito cewa, Bashir Baffa ya ƙara da cewa a shirye gwamnatin jihar Kano, take wajen ci gaba da kula wa da karatun ɗalibai a faɗin jihar, domin sauƙaƙa musu tare da samun ingantaccen ilimi.
