Koma Labarai
Addini

Hukumar Shari'a ta saɓunta kwamitocin ta don ƙara ciyar da addini, da al'umma gaba a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta saɓunta kwamitocin ta don ƙara ciyar da addini, da al'umma gaba a Kano.

Hukumar Shari'ar addinin Musulunci ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta saɓunta kwamitocin ta daga huɗu suka zuwa biyu, da suka haɗar da kwamitin Sulhu, da na tantance Limaman masallatai, domin ƙara ciyar da addini, da ma al'umma gaba ta ɓangarori daban-daban.

Da yake ƙaddamar da saɓunta kwamitcocin, Kwamishina na biyu a hukumar Shari'ar, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya shaidawa Dala FM Kano cewa, an saɓunta kwamitocin ne bisa sahalewar shugaban hukumar Sheikh Ali Ɗan Abba, bisa irin gudunmawar da suke bayar wa ga jama'a.

Sheikh Ɗan Abba, ya kuma buƙaci shugabannin kwamitocin da su dage wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora musu yadda ya kamata, domin ƙara ciyar da addini, da ma al'umma gaba.

A cewar sa, mambobin kwamitocin da aka saɓunta an samar da su ne daga Mambobi a hukumar gudanarwar hukumar Shari'ar ta Kano, da kuma Daraktoci a hukumar, bayan da aka rushe na baya.

Da suke nasu jawaban daban-daban, shugaban kwamitin tantance Limamai, Sheikh Muhktar Mama Ali, da ya samu wakilcin Sakataren kwamitin Muhammad Abu Musa, da shugaban kwamitin Sulhu, Mallam Ibrahim Inuwa, sun ce za su yi aiki tuƙuru domin samar da ci gaban da ya dace a aikin da aka ɗora musu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM